Ministan tsaron Nijeriya, Abubakar Badaru, ya sauya matsayarsa ta da cewa ba ya goyon baya gan taron koli na tsaro da majalisar tarayya ke kokarin shiryawa.
Minista Badaru ya ce wannan taro da majalisar ke kokarin shiryawa zai zo ne a lokacin da ake bukatarsa. Badaru ya sha alwashin halartar wannan taro na kwanaki biyu da kuma tabbatar da cewa sakamakon taron zai haifar da da mai ido.
Sabon matsayin ministan na nuni da sabani da kalamansa na ranar Laraba a yayin wani taron bayani tsakanin ministoci, inda ya ce tsara wata sabuwar dabarar tsaro zai fi amfani fiye da kiran taron koli.