Dame Patience Jonathan, uwargida ga tsohon shugaban Nijeriya Good Luck Ebele Jonathan ta jaddada aniyarta cewa ba za ta koma fadar shugaban kasa ba ta Aso Villa Abuja ba.
Wadannan kalamai nata na fitowa ne a lokacin da take cewa za ta hadu uwargidan Shugaba Tinubu, wato Oluremi Tinubu su yi kyamfen don APC ta sake lashe zabe a 2027.
Dame Patience ta ce tsarin karba-karba da ake yi a Nijeriya yana haifar da da mai ido.