DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ana fama da karancin ayyukan yi a Ingila

-

Matsalar rashin aikin yi a Birtaniya ta kai matsayi mafi tsanani tun watan Agustan shekarar 2021, a cewar bayanan hukuma da aka fitar, yayin da kamfanoni ke fuskantar karin haraji daga gwamnati da kuma harajin fito da kaya daga Amurka.

Ofishin kididdiga na kasa ONS ya bayyana cewa adadin marasa aikin yi ya karu zuwa kashi 4.5% a watanni uku na farko na shekara.

Google search engine

Wannan ya karu daga kashi 4.4% da aka samu a watannin uku da suka kare zuwa karshen Fabrairu, in ji ONS.

Bayanan sun shafi lokacin kafin a fara aiwatar da karin harajin kasuwanci da aka sanar a kasafin kudin farko na gwamnatin jam’iyyar Labour a watan Oktoba.

Haka nan kuma, bayanan sun riga lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba harajin kashi 10% kan kaya daga Birtaniya da wasu kasashe a bara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara