DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Donald Trump ya kai ziyarar aiki a Saudiyya

-

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa Saudiyya a wata ziyara ta kwanaki hudu a yankin Gulf mai arzikin man fetur, inda zai mayar da hankali kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da batutuwan tsaron yankin.

Batutuwan sun hada da yakin Gaza da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran.

Google search engine

Trump na tare da fitattun shugabannin kasuwanci daga Amurka a ziyarar, inda zai fara da ziyartar Riyadh, inda ake gudanar da taron Saudi-U.S. Investment Forum, kafin ya wuce Qatar ranar Laraba da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa ranar Alhamis.

Ba ya da shirin tsayawa a Isra’ila, abin da ya tayar da tambayoyi game da matsayin wannan kasa abokiyar Amurka a cikin jerin fifikon siyasar Amurka.

Trump na fatar samun zuba jari na tiriliyoyin daloli daga kasashen da ke samar da mai a yankin Gulf.

Saudiyya ta yi alkawarin zuba jarin Dalar Amurka bilyan 600, amma Trump ya bayyana cewa yana son dala tiriliyan 1 daga Saudiyya, wadda ke daga cikin manyan abokan huldar Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara