Hukumomin mulkin sojan Nijar sun tusa kewar ‘yan jaridar uku na Radio Sahara da suka kama a Agadez zuwa babban birnin Yamai.
Jami’an tsaron Gendarmerie na jihar Agadez sun yi wa ‘yan jaridar uku na Radio Sahara rakiya zuwa babban birnin Yamai bayan sun kwashe kwanaki hudu a tsare a hannun gendarmerie.
‘Yan jaridar dai uku da suka hada Hamid Mahmoud, Masaouda Jaharou da kuma Mahaman Sani an kama su ne da farko a daren 7 wayewar 8 ga watan Mayun nan biyo bayan yada wani labari da ke nuna cewa Nijar ta katse dangantakar tsaro da kasar Rasha.
An dai kuma saki ‘yan jaridar a ranar 9 ga watan Mayun bayan an gurfanar da su a gaban kotun jihar Agadez sai dai a daren wannan rana ta 9 wayewar 10 ga watan Mayun kuma jami’an tsaron Gendarmerie sun sake kama su da misalin karfe 3 na dare inda suka shafe kwanaki 4 kafin a yau a tusa kewar su zuwa babban birnin Yamai.