By Salim Muhammad Gali
Babban bankin Nijeriya CBN tare da haɗin gwiwar Hukumar NIBSS da ke kula da harkokin bankuna a Nijeriya sun ƙaddamar da sabon tsarin da zai bai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen ƙetare damar samun BVN ba tare da sun koma gida Nijeriya ba.
Gwamnan Babban bankin kasar CBN, Olayemi Cardoso, ne ya ƙaddamar da shirin a Abuja.
Cardoso ya bayyana cewa tsarin zai sauƙaƙe tare da ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗin Najeriya, hakam ana hasashen tsarin za a yi hada-hadar da ta kai dala bilyan 1 a kowane wata.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa sabon tsarin zai ba da damar rijista ta yanar gizo ta amfani da fasahohin zamani kamar tantance fuska, takardun shaidar zama ɗan Najeriya da sauran matakan tsaro, tare da tabbacin kariyar bayanai.