Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kaura Namoda da Birnin Magaji a jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ke addabar yankin Arewa maso Yamma sun ba karnukansu wasu jarirai ‘yan biyu da aka haifa a lokacin da Barau n dajin ke tsare da mahaifiyarsu.
Yayin wata tattaunawa da manema labarai, Jaji ya ce an sace wata mata daga wani gari a jihar Zamfara tana dauke da juna biyu.
Ya ce bayan da matar ta haifi ‘yan biyu, sai ‘yan bindigar suka jefa jariran ga karnuka, inda suka cinye su.
Hon Sani Jaji ya ce wannan shi ne matakin rashin imani da rashin tausayi da yankin ke fama da shi.