Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wani shugaban jam’iyyar APC na gundumar Ward 5 da ke Ifon, a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Nelson Adepoyigi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a bakin gonarsa da ke kan hanyar Ifon zuwa Owo.
Majiyoyi daga cikin al’umma sun ce ‘yan bindigar sun tuntubi iyalan wanda aka sace, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100 kafin su sako shi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, DSP Olusola Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai a Akure, babban birnin jihar.