By Salim Muhammad Gali
Shugaban darikar Roman Katolika, Fafaroma Leo 14 ya bayyana cewa a shirye yake ya taimaka wa shugabannin ƙasashe masu fama da rikici wajen tattaunawa don samar da zaman lafiya.
Sabon Fafaroman, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake jawabi ga mambobin Cocin Katolika a fadar Vatican, inda ya roƙi Kiristoci dake yankin Gabas ta Tsakiya da kada su bar muhallansu.
Fafaroma ya ce “jama’ar duniya na marmarin zaman lafiya, don haka nake roƙon shugabanninsu da zuciya ɗaya: mu zaina mu tattauna, mu cimma matsaya! don kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe.”