Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta shawarci mahajjatan kasar da su guji daukar kudi sama da Riyal 60,000 na Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin 2025.
Hukumar NAHCON ta bayar da wannan shawara ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Shafil Mohammed, ya fitar a Abuja.
Mohammed ya gargadi mahajjata da su guji daukar makudan kudade a jikinsu.