Kamfanin Orano na kasar Faransa mai aikin hakar ma’adanan uranium a Nijar ya ce ya garzaya kotu domin domin kalubalantar kamun da gwamnatin Nijar ta yi wa wani babban jami’in kamfanin a ofishinsa da ke a birnin Yamai.
Kamfanin dai ya bayyana hakan ne a ranar 13 ga watan Mayun nan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shainsa na yanar gizo, inda ya ce wannan kamu ya saba doka.
A cewar kamfanin tun a ranar 5 ga watan Mayu ne wasu jami’an tsaro suka kutsa ofisoshin ma’aikatansa suka kwashe na’urorin komfutoci tare da kwace wayoyin ma’aikatan.
Kamfanin ya kara da cewa, a yayin wannan samame ne da jami’an tsaron suka yi awon gaba da babban daraktan kamfanin Orano Malan Ibrahim Courmo kuma har yanzu kamfanin bai samu damar yin magana da shi ba, tsawon kwanaki takwas kenan ake tsare da shi.
Kazalika kamfanin ya ce a yanzu haka jami’an tsaron sun yi wa ofishin kamfanin kawanya.
Tun bayan juyin mulkin Yulin 2023 dai ake ta kai ruwa rana tsakanin kamfanin Orano da hukumomin mulkin sojan Nijar.