By Salim Muhammad Gali
Ministan wutar lantarki na kasa Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Nijeriya na buĆ™atar aĆ™alla dala biliyan 10 duk shekara na tsawon shekaru 20, domin samar dai isashshen wutar lantarki ga ‘yan kasar.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan na wannan bayanin, a yayin da yake kaddamar da tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana mai ƙarfin megawat 2.5 a makarantar sojoji NDA da ke jihar Kaduna.
Ministan ya ce sama da shekaru 60 matsaloli sun dabaibaye bangaren lantarki da suna hada rashin isasshen saka hannun jari, rashin kiyaye kayayyakin aiki, da kuma ƙarancin inganta tsarin rarraba wutar.
Adelabu ya bayyana cewa sanya hannu kan dokar makamashi ya bai wa jihohi damar taka rawa kai tsaye a harkar samar da wuta, kama daga samarwa zuwa rabawa, kuma fiye da jihohi 11 sun fara daukar hanya.