Wasu daga cikin daliban da suka rubuta jarabawar JAMB da ke ba da damar samun gurbin karatu a manyan makarantun gaba da sakandare ta shekarar 2025 sun bukaci a soke sakamakon jarabawar gaba daya.
Sun bayyana hakan ne a hirarsu da jaridar Daily Trust, a martaninsu ga amincewar Hukumar JAMB cewa an samu kura-kurai da suka shafi yadda dalibai suka fuskanci jarabawar.
An sha korafe-korafe daga sassa daban-daban na Nijeriya game da rashin kyakkyawan sakamako, inda sama da dalibai milyan 1.5 suka kasa samun maki 200. Wasu sun danganta hakan da matsalolin fasaha a wasu cibiyoyin jarabawa, yayin da wasu ke zargin rashin tsara lokaci da kuma rashin isasshen shiri daga bangaren dalibai.
Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya fashe da kuka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, yayin da yake bayar da hakuri kan kura-kuran da suka shafi jarabawar.