Kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna karkashin mai shari’a R.M. Aikawa ta yanke wa wani dan TikTok da Instagram, Muhammad Kabir, hukunci bayan samunsa da laifin wulakantawa da lalata takardun kudi na Naira.
A cewar Shugaban Sashen Yada Labarai na hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Nijeriya, Dele Oyewale, an kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Mayu, 2025 a Tudun Wada, Jihar Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo a shafukan sa na TikTok da Instagram mai dauke da sunan @youngcee0066, inda aka gan shi yana watsi da takardun Naira a kasa, yana tattakawa, tare da fadin wasu kalamai a harshen Hausa yana kalubalantar EFCC da ta zo ta kama shi a inda yake.
An kama shi ne bisa karya dokar babban bankin Nijeriya CBN wadda ta haramta wulakantawa da lalata takardun kudi na Naira.
Alkalin kotun, Mai shari’a Aikawa, ya yanke wa Muhammad hukuncin dauri na wata shida 6 ko kuma ya biya tara ta Naira Dubu Dari Uku N300,000.00 ga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.



