Fitaccen mawakin nan na kudancin Nijeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya ce shi ne shahararren dan Nijeriya da ya fi fuskantar suka, duba da inda ya fito.
Da yake magana a shirin Culture Knock Out podcast, mawakin ya bayyana cewa ra’ayin jama’a ya canza ne bayan an gano cewa ya fito daga gidan masu kudi.
Davido ya ce, da al’umma sun san asalinsa tun farko, da hakan na iya shafar yadda ya kai ga samun nasara a halin da ake ciki.
Davido ya kara da cewa sukar da jama’a ke yi masa, yawanci tana tafiya ne da nasara.