Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa jami’anta, sun kama wata mata da ake zargi da safarar makamai ga barayin daji.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Namsel ya ce, an kama Fatima Salisu mai kimanin shekaru 21 ‘yar asalin garin Funtua da ke a jihar Katsina bayan samun bayanan sirri a yankin Azuba da ke a Lafia.
Ana zargin Fatima ne da safarar albarusai daga jihar Nasarawa zuwa ga wasu barayin daji a Jihar Katsina.
Yanzu haka dai, wacce ake zargin na hannun jami’an tsaro domin ci-gaba da bincike da tuhumarta don gano wadanda ke da alaka da makaman.