Dakarun runduna ta 6 ta sojin Nijeriya na Operation WHIRL STROKE tare da hadin guiwar dakarun aikin SAFE HAVEN, sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kwato shanu dubu guda 1,000 da aka sace a jihar Taraba.
Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Capt Oni Olubodunde, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce nasarar kashe ‘yan bindigar da kuma kwato shanun ya samu ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu.
Ya ce yayin arangamar, dakarun sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kwato shanu kimanin 1,000 da aka sace.
An garzaya da shanun da aka kwato zuwa wuri mafi aminci, inda daga nan aka kai su kauyen Jebjeb da ke karamar hukumar Karim Lamido.