Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta bayyana cewa mahajjatan kasar 20,515 suka isa kasar Saudiyya a cikin mako daya.
Jami’in yada labaran hukumar Malam Shafil Mohammed ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da ya ke karin bayani game da yadda jigilar mahajjatan 2025 ke gudana.
Mohammed ya kara da cewa, a cikin mako daya, jirage 50 ne suka yi jigilar mahajjata 20,515 zuwa kasar Saudiyya.