Dattijo a Nijeriya, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce a halin yanzu, babu wanda ke da damar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
Yakasai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN a Abuja.
Haka kuma ya ce, duk da kasancewarsa daya daga cikin manyan mambobin Kungiyar Tuntuba ta Arewa Arewa Consultative Forum, bai san da wani taro ko dandalin da Arewa ta yanke shawarar mara wa wani dan takara daga yankin baya a zaben 2027 ba.
Yakasai ya ce baya ga jam’iyyar APC mai mulki da ke rike da mafi yawan jihohi a kasar, akwai wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa da har yanzu ke goyon bayan Tinubu.
A cewarsa, rikicin da ke addabar wasu daga cikin manyan jam’iyyun adawa ya kara bude kofar cin nasara ga Tinubu a zaben 2027.