Rahotanni sun tabbatar da cewa masu garkuwa sun kashe shugaban jam’iyyar APC na mazabar 5, Ifon, a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, bayan sace shi a gidansa da ke Ifon kwanan nan.
Masu garkuwar sun fara Neman kudin fansa Naira milyan 100, amma daga bisani bayan tattaunawa suka rage kudin zuwa Naira milyan 5 tare da kayan abinci.
Haka kuma, sun kama wasu mutane biyu da suka kai kudin fansar, inda suka nemi sabon kudin fansa Naira milyan 30 domin sakin mutum ukun da ke hannunsu, ciki har da Adepoyigi da waɗanda suka kai kudin fansar.
Shugaban karamar hukumar Ose, Barr Clement Kolapo Ojo, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Oluwaseun Ogunniyi, ya fitar.