Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana wanda ya gada a mulki, Siminalayi Fubara, a matsayin “yaronsa,” a yayin da rikicin siyasa ke ci gaba tsakaninsu.
Wike, wanda yanzu haka shi ne ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce ko da yake Shugaba Bola Tinubu ya nemi zaman lafiya, bai yi adawa da hakan ba.
Ya ce wannan yaro nawa ne, dana ne. Yaya zan ce ina yaki da shi? Wadanda nake fada da su, su ne masu kokarin sace abin da ba su yi aiki akai ba.
“Shugaban kasa ya kira ni domin a samu sulhu; na ce masa, ‘Oga, ta yaya zaka ce in sasanta, amma in ki?’” in ji shi a wata hira da ya yi da BBC Pidgin.