Wani bincike da kungiyar ActionAid ta gudanar ya nuna cewa Nijeriya na iya yin asarar Naira Tiriliyan 60 a duk shekara sakamakon rashin tallafa wa matasa a fannin noma da gangan.
Jami’in kungiyar ActionAid a Nijeriya, Azubike Nwokoye ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da ya ke gabatar da makala kan shirin samar da fasahar noma na matasa a Nijeriya (NYAIP) a taron tattaunawa kan tsarin samar da abinci ga matasa na kasa, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar kwamitin majalisar dattijai kan harkokin noma da tallafawar kungiyar hadin gwiwar kasa da kasa ta Jamus (GIZ) ta yi.
Azubike ya bayyana cewa, idan aka tallafa wa matasa marasa aikin yi kusan miliyan 40 a Najeriya a fannin noma, hakan na nufin za a samar da sabbin ayyukan noma kusan miliyan 40 kuma idan kowane matashi ya ba da gudummawar kusan dalar Amurka 1,000 ga tattalin arzikin Nijeriya a duk shekara, zai kai dala biliyan 40 a duk shekara.
Ya ce ko da matasa miliyan biyar ne kawai aka ba su damar yin noma a Nijeriya, darajar kudin da za a kara wa tattalin arzikin kasar ta yarjejeniyar AFCFTA na iya kaiwa tsakanin dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 20 a duk shekara.