Akalla mutane uku ne rayukansu suka salwanta aka kuma sace wasu 26 a wani sabon harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ce hare-haren da aka kai tsakanin ranakun Alhamis da Asabar, sun shafi mutane da dama.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa kauyen Sabon Gari sun sha fama da tashin hankalin na baya-bayan nan, inda aka halaka mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20.
Wani mazaunin Kauran Namoda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa adadin ya zarta haka, inda ya ce an kashe mutane hudu, ciki har da mace daya, tare da sace wasu 26.
Rahotanni sun ce daga cikin wadanda aka sacen har da wani mutum, da matansa biyu, da ‘ya’yansu uku.