Tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Nijeriya, Olisa Agbakoba SAN, ya bayyana cewa tsarin dimokuraɗiyyar da Najeriya ke amfani da shi wanda aka aro daga ƙasashen Yamma ba ya aiki, yana mai kira da a sake fasalin tsarin mulkin.
A cewarsa, bayan fiye da shekara 25 da mulkin dimokuraɗiyya, har yanzu Najeriya ba ta samu cigaba mai ma’ana ba, yana mai cewa akwai babban kuskure a tsarin da ba ya samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan ƙasa.
Agbakoba ya soki yadda ‘yan adawa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yana cewa hakan ba zai taimaka wajen gyara demokaraɗiyya ba. Inda yace da yawa cikin ‘yan siyasa burinsu kawai shi ne su karɓi mulki, ba kula da bukatun talakawa ba.