Mambobin kungiyar kwadago ta TUC sun gudanar da zanga-zanga a ma’aikatar kudi ta tarayya da ke Abuja a ranar Talata, don nuna bacin ransu kan rashin walwalar ma’aikata, bashin albashi da alawus da ake bin su.
A cewar jaridar Punch, masu zanga-zangar da ke sanye da jajayen riguna dauke da alluna, sun rufe kofar shiga da fita ta ma’aikatar, tare da hana ababen hawa wucewa, lamarin da ya tilasta wa wasu ma’aikatan komawa gida.