Wani rahoton jaridar Dailytrust ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na shirin zama sabuwar cibiyar hadin gwiwar manyan ‘yan adawa a Najeriya, bayan da aka amince da ita a matsayin dandalin fafutukar siyasar da za ta kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Wannan hadaka karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a 2023 Peter Obi, da kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ta samu ne bayan ganawar sirri da aka yi a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa, tun da farko hadakar ta yi shirin amfani da jam’iyyar SDP, amma rikicin cikin gida da rashin yarda da sharudan da jam’iyyar ta gindaya ya sa aka fasa hakan.
Shugaban SDP, Shehu Gabam, ya bayyana cewa ba za su bari a tasirinsu ya zama na wucin gadi ba, daga ADC kuwa shugabanta Ralphs Nwosu, ya tabbatar da tattaunawa da kwamitin hadakar, yana mai cewa hadin gwiwar na neman ceto Najeriya daga halin da take ciki.