By Salim Muhammad Gali
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS hadin gwiwa da ‘yan sandan Najeriya sun cafke wasu mutane 20 a Abuja, bisa zargin su da kutse a sakamakon jarabawar JAMB ta shekarar 2025.
Hukumar DSS da ’yan sanda sun bayyana cewa mutanen da aka kama na daga cikin wasu gungun masu laifi da ake zargin sun fi mutum 100, wadanda suka kware wajen kutsawa cikin kwamfutocin cibiyoyin shirya jarabawa kamar JAMB da NECO domin sauya sakamako ko yin damfara.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa wadanda aka kama sun aikata wannan laifi ta hanyar kutse a cibiyar na’urorin JAMB lokacin da ake zana jarabawar bana.



