Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya musanta zargin yi wa jam’iyyar APC mai mulki aiki domin ruguza jam’iyyar PDP.
Damagum ya kuma kare alakarsa da tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, biyo bayan sukar da wasu ‘yan jam’iyyar suka yi masa na cewa yana hada kai da Wike domin ruguza jam’iyyar PDP.
A wata hira da ya yi da manema labarai, Damagun ya kara tabbatar da biyayyarsa ga jam’iyyar PDP, inda ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofin jam’iyyar.



