Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wata matar aure mai suna Zaliha Shuaibu bisa zargin kashe jaririn kishiyarta dan watanni uku ta hanyar ba shi guba a kauyen Malari da ke karamar hukumar Soba ta jihar.
Wannan lamari ya faru ne a ranar 13 ga Mayu, 2025, a cikin gidan da suke zaune tare da mahaifiyar jaririn, Maryam Ibrahim.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito, inda ya ce an kama wadda ake zargin ne bayan binciken gaggawa da jami’an ‘yan sanda na Sashen Soba suka gudanar.



