Majalisar dokokin jihar Katsina ta sanar da cewa ta aminta Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ya nemi tazarce a zaben shekarar 2027 mai zuwa.
Kazalika, ‘yan majalisar dokokin sun kuma yi alkawarin za su saya wa Gwamna Radda “form” din takarar wa’adi na biyu idan har bukatar hakan ta taso.
Kakakin majalisar dokokin Nasiru Yahaya Daura ya ce madadin daukacin ‘yan majalisar su 34, sun yanke wannan shawarar ne bayan sun yi la’akari da irin cigaban da Gwamna Radda ke kokarin kawo wa jihar Katsina.



