Jam’iyyar PDP ta dage zaman taronta karo na 99 na kwamitin zartarwa na kasa NEC.
A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu ya sanya wa hannu, PDP ta bayyana cewa an dage taron ne domin ba wa kwamitin sulhu da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ke jagoranta damar kammala aikinsa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an shirya gudanar da taron NEC din ne a ranar 27 ga Mayu, 2025, a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja.