Sha’anin tsaro na ƙara tabarbarewa a Najeriya, inda a makon da ya gabata aka hallaka akalla mutane 95 tare da yin garkuwa da wasu 68 a fadin kasar.
Binciken jaridar Premium Times ya gano cewa waɗannan alkalumman sun fi na makon da ya gabata, sanadiyar hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda.
An yi wannan bincike ne daga labarai da kuma rahotannin kafofin sadarwa tsakanin 17th zuwa 23 ga Maysecuritysecurityu.
Rahoton ya gano cewa su ma hukumomin tsaro sun samu nasarori a makon da ya gabata.