Hukumomi a birnin Sabha na kasar Libya sun kama wasu ‘yan Najeriya biyar da ake zargi da satar kayan lantarki a wata gona.
Kungiyar Migrant Rescue Watch ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a shafukan sada zumunta a ranar Litinin, 26 ga Mayu, 2025.
A cewar rahoton, jami’an hukumar ‘yan sanda ta Al-Qahira ne suka cafke wadanda ake zargin a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayu, kuma tuni an miƙa su ga sashen shari’a domin daukar mataki na gaba.