Hukumar kula da ruwa ta babban birnin tarayya Abuja ta sanar da cewa za a samu tsakon samar da ruwan sha a babban birnin tarayya nan da makwanni biyu masu zuwa.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa za a fuskanci matsalar samar da ruwa a tsakiyar birnin da kuma bayan gari ne sakamakon aiki gyaran madatsar ruwa ta gundumar Usuma.
Hukumar ta ce aikin na gyare-gyaren zai bada damar hada na’urorin da lantarki wadanda ke taimakawa wajen samar da ruwan.