Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce yana samun farin ciki duk lokacin da ya takalo manyan mutane a kasar.
Wike, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, ya ce duk masu kadarorin da ke Abuja da har yanzu ba su biya harajin kasa na gidansu ba, inda ya kara da cewa dole ne su yi hakan ko kuma su fuskanci fushin doka.
Tsohon gwamnan jihar Ribas ya caccaki wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da Bode George, yana mai cewa dole ne PDP ta biya harajin ofishinta da ke Abuja.
Wike ya ce magabatansa da suka jagoranci babban birnin tarayya Abuja ciki har da gwamnan jihar Bauchi a yanzu Bala Mohammed, sun kasa tilasta jiga-jigan ‘yan siyasa wadanda suka mallaki gine-gine a Abuja su rika biyan kudin harajin gidajensu na shekara-shekara.