Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta ce kasar Saudiyya ba ta amsa rokonsu na sake bude damar samun visar aikin hajjin 2025 ba.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce tana mai bai wa mutanen da abin ya shafa hakuri. Hukumar ta ce duk wanda bai samu visar ba ya tuna cewa hajji kiran Allah ne, ta ce tana shawartar nan gaba mahajjata su rika biyan kudi a kan kari domin guje wa fadawa irin wannan yanayi.
Fatima Sanda Usara wadda ta fitar da sanarwar ta ce hukumar NAHCON ta roki Saudiyya da ta tsawaita wa‘adin rufe bayar da visar a 29/04/2025 kuma Saudiyyar ta bude har zuwa ranar 19/05/2025 da ta rufe kuma ba ta sake budewa ba duk da rokon da NAHCON ta yi.