Takaddama ta kunno kai a cikin jam’iyyar APC a Jihar Filato dangane da kiran da wani rukuni ya yi cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Wani rukunin APC na Arewa ta Tsakiya mai suna North-Central All Progressives Congress Forum karkashin jagorancin Saleh Zazzaga ya mara wa Mutfwang baya don ya sake neman wa’adi na biyu, inda suka nemi ya shiga jam’iyyar APC, suna mai cewa ya nuna bajinta a aikinsa kuma manufofinsa na tafiya da na Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai wata kungiya mai suna APC Like Minds Political Forum ta fito fili ta soki wannan kira, inda ta bayyana shi a matsayin “kira mai hatsari, cike da kiyayya kuma na son rai.”
A wata sanarwa da ya fitar, Zazzaga ya ce an yanke shawarar mara wa Mutfwang baya ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa rukunin ya amince da Green Cap Movement, wata tafiya da ake dangantawa da gwamnan, a matsayin wata manufa da za su bi a zaben gwamnan 2027, tare da sake nuna goyon bayansu ga Shugaba Tinubu don ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
Amma kungiyar APC Like Minds Political Forum ta maida martani a cikin wata sanarwa da Habibu Musa Sati ya fitar kuma aka rabawa manema labarai, inda ta ce abin da Zazzaga ke yi wata dabara ce da za ta hana APC sake farfadowa da bunkasa a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa jam’iyyar APC tana da mutane masu cancanta da kwarewa da za su iya jagorantar Jihar Filato a shekarar 2027.
Kungiyar ta kuma kalubalanci sahihancin Zazzaga, inda ta bayyana cewa bai zabi APC ba a zaben da ya gabata, kuma yana da tarihin rikice-rikice da ke sa shakku a gaskiyarsa da amincinsa.