DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fursunoni 200 sun arce daga gidan yarin kasar Pakistan

-

Jami’ai a kasar Pakistan sun bayar da rahoton cewa fiye da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari a birnin Karachi bayan da aka bar su su fita daga dakunansu sakamakon girgizar kasa da aka ji sau da dama a yankin.

Zia-ul-Hasan Lanjar, kwamishinan shari’a na jihar, ya shaida wa ’yan jarida a wurin cewa an bai wa daruruwan fursunoni damar fita zuwa harabar gidan yari saboda girgizar kasar.

Google search engine

Farkon tserewar fursunonin ya faru ne da daren Litinin kafin karfe 12 na dare, kuma ya ci gaba har zuwa wayewar garin Talata, in ji kwamishinan.

’Yan sanda sun ce fursunonin sun kwace bindigu daga hannun ma’aikatan gidan yari, abin da ya janyo musayar wuta, kafin daga bisani su tilasta a bude kofar shiga ta gaba.

A ranar Talata, wani wakilin kamfanin Reuters da ke wurin ya ga tagogi fasassu da kuma na’urorin lantarki da suka lalace a cikin gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rigimar Naira 8,000 ta janyo ajalin wani dan tireda a kasuwar Lagos

Ƙarin bayani ya fito kan rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani ɗan kasuwa, Sodiq Ibrahim, a yankin Mandillas na tsibirin Lagos a ranar Laraba. Binciken...

Trump ya soke tallafin ketare na dala biliyan 5 a kasafin kudin Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauki matakin dakatar da dala biliyan 5 na tallafin ƙasashen waje da majalisar dokokin ƙasar ta riga ta amince da...

Mafi Shahara