DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda sun kama mutumin da ake zargi da keta haddin ‘agolarsa’ a Bauchi

-

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun samu nasarar dakile wani yunkurin kai hari da matasa suka shirya yi wa wani mutum mai shekaru 37 da haihuwa da ake zargi da cin zarafin diyar matarsa wato ‘agolarsa’ mai shekaru 15.

A cewar rundunar, jami’an da ke karkashin shirin “Operation Restore Peace” wanda CSP Kim Abert ke jagoranta, sun samu bayanan sirri masu inganci wanda ya ba su damar dakile harin da ake shirin kai wa mutumin mai suna Wisdom Benoie.

Google search engine

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Bauchi.

Sanarwar ‘yan sandan ta ce binciken farko-farko sun bayyana cewa mutumin na auren mahaifiyar budurwar ne. Wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yawaita buga sabbin takardun kudi da da aka rika yi a gwamnatin Buhari ne ya gurgunta darajar Naira – Oshiomhole

Sanata Adams Oshiomhole, ya zargi tsohuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da taka raws wajen gurgunta tattalin arziki Nijeriya Ya bayyana hakan a wani taro...

Murabus din Ganduje wata maƙarƙashiya ce aka shirya domin cire Shettima daga gwamnatin Tinubu – Zargin wasu mutanen Borno

Wasu daga cikin al'ummar jihar Borno sun zargi murabus din Ganduje a matsayin wata maƙarƙashiya da aka shirya domin a kawar da Kassim Shettima a...

Mafi Shahara