Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta haramta wa ‘yan kasashe 12 shiga Amurka.
Kasashen da abin ya shafa sun hada da Afghanistan, Myanmar, Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan da Yemen.
Duk wani dan ƙasa daga waɗannan ƙasashe za a hana su cikakkun takardun shiga Amurka, kamar yadda sanarwar ta ce.
Kazalika, za a takaita shigar ‘yan kasashen Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da Venezuela.
Trump ya ce ana bukatar daukar matakin ne domin kare Amurka daga ‘yan ta’adda na kasashen waje da sauran barazanar tsaro.