Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna ta yi tir da sabbin hare-haren ‘yan bindiga a jihar inda ta bayyana hakan a matsayin abin takaici da kuma gazawar gwamnati.
PDP ta ce, harin da aka kai a kauyukan Kagara da Ugom da ke kananan hukumomin Giwa da Kajuru sun yi sanadiyar rasa rayukan mutane 2 da jikkata wasu tsakanin 4 zuwa 6 ga watan Yuni,2025.
A bayanin da jam’iyyar ta fitar a ranar Asabar wanda ke dauke da sa hannun Shugaban jam’iyyar na Jihar Kaduna, Edward Masha ya nuna bakin cikinsu na rasa rayukan da halin da iyalan mamatan za su shiga.
Jam’iyyar ta yi kira ga gwamnatin Uba Sani da su gaggauta bitar tsarin tsaron jihar musamman ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar da su falka daga bacci don sauke nauyin da ke a wuyansu.



