Wani mutum ya afka cikin rijiya bayan da ya yi mankas da kayan maye a jihar Kwara
A ranar Asabar ne hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara ta ciro gawar wani dan shekara 43 a cikin rijiya bayan ya yi mankas da kayan maye a garin Edun da ke Karamar Hukumar Ilori ta kudu.
Ana zargin mamacin mai suna Kareem da yin mankas da wata kwaya da ake Kira “Colorado” wajen murnar babbar sallah, inda ya yi tsalle ya fada rijiya Jim kadan bayan dawowa daga sallar Idi a ranar Juma’a.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma samo gawar mamacin.



