‘Yan sanda a jihar Neja sun cafke wani mai suna Mohammed Sani da ke a rukunin gidajen Banin Hashim a Minna bisa zargin dukan matarsa, Hauwa har lahira.
Mohammed, mai kimanin shekaru 31, ya bugi matarsa, Hauwa ‘yar shekara 24 har lahira da ciki wata 9.
Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar ma jaridar Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce, a ranar 3 ga watan Yuli suka samu Kira daga rukunin gidajen da misalin karfe 10:30 na dare. Zuwa su ke wuya suka tarar da gawar matar kwance cikin jini.



