DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NAPTIP ta kubutar da ‘yan Nijeriya 20 da aka yi safarar su

-

Hukumar yaki da safarar mutane ta Nijeriya NAPTIP, haɗin guiwa da hukumar tsaro ta DIA, sun kubutar da mutane 20 daga gungun masu safarar mutane da ke aiki a ƙasashen Equatorial Guinea da Togo da kuma Najeriya.

Jami’an NAPTIP sun bayyana cewa waɗanda aka ceto an yaudare su da alkawarin samar musu ayyuka masu albashi mai tsoka, sai dai daga bisani aka tilasta musu yin aikin karfi.

Google search engine

Jami’in hulɗa da jama’a na NAPTIP, Vincent Adekoye, ya ce an kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a safarar a Abuja, Osun da Nasarawa, yayin da hukumar ta ƙara sa ido a kan iyakokin ƙasa don hana safarar mutane.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu is a highly skilled and experienced broadcast journalist and fact-checker. Ukashatu has over five years of experience in writing, editing, and presenting news and program content for radio and television. As a dedicated and hardworking professional, He is committed to upholding the values of accuracy, fairness, balance, independence, and accountability in her reporting and programs.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 53 kan tagwayen hari a jihohin Benue da Filato – IGP Egbetokun

Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutane 53 da ake zargi da hannu a hare-haren da suka yi...

Kiran kungiyar NNPYA na neman Tinubu ya zabe ni a takarar mataimaki a 2027 bai dace ba yanzu – Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya ce kiraye-kirayen da kungiyar matasan jam’iyyar APC na Arewa (NNPYA) ke yi na a zabe shi...

Mafi Shahara