Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kare aikin da yayi na zunzurutun kudi har biliyan 39 wajen gyaran dakin taron kasa da kasa da ke Abuja.
Ministan, ke jawabi a yayin kaddamar da wata sabuwar hanyar a Abuja, ya ce komai sai da aka canza a cikin dakin taron in ban da gini.
Wike ya ce duk da cewa an kashe Naira Milyan 240 wajen gina dakin taron a shekarar 1991, amma yanzu an samu sauyi sosai a farashin kayayyaki, wanda ya sa aka kashe Naira Bilyan 39 wajen gyaran dakin taron na kasa da kasa.
Ministan Abuja ya ce wadanda ke suka kan yawan kudaden da aka kashe ba su san abinda suke yi ba.