Gwamnatin jihar Sokoto ta kare matakin da ta dauka na neman yin sulhu da ‘yan bindiga da suka amince da ajiye makamansu, inda ta bayyana hakan a matsayin mafita mai dorewa ga matsalar tsaro a jihar.
Gwamnatin na mayar da martani ne kan kalaman da wani mai sharhi kan shafukan sada zumunta, Basharu Altine Guyawa ya yi, wanda ya soki matakin.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya ya fitar, ya ce ba rauni ne ya sa gwamnati neman sasanci ba.