Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira ta kasa ta ce ‘yan Nijeriya sama da 250,000 ke gudun hijira a Libya, Sudan ta Kudu, Kamaru, Chadi, Nijar da wasu sassan duniya.
A gefe daya kuma akalla ‘yan gudun hijira 135,000 daga kasashe daban-daban ke zaune a Nijeriya.
Hukumar ta bayar da wannan adadi a jiya bayan wata tattaki da ta yi a Abuja domin tunawa da ranar ‘yan gudun hijira ta duniya ta 2025.
Kwamishinan hukumar na tarayya, Tijani Ahmed, wanda ya bayyana cewa gaga cikin ‘yan gudun hijira 250,000 na Nijeriya, 125,000 suna zaune a Kamaru.