Tsohon mai bai wa shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya musanta ikirarin da ake yi na cewa ‘yan siyasar Arewa ne ke jagorantar kawancen da ke adawa da gwamnatin Tinubu.
Da ya ke magana a gidan talabijin na Arise a Litinin dinnan Hakeem Baba-Ahmed, wanda a kwanakin baya ya yi murabus daga mukaminsa, ya bayyana cewa kawancen da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ke jagoranta, ba shiri ne na yankin Arewa kaɗai ba.
Ya ce hadakar ‘yan siyasa ba sabon abu bane a Nijeriya, inda ya ce duk hadakar da ta faru a kasar ta shafi ‘yan kuduncin ƙasar.
A cewar sa akwai ‘yan Kudu da ke cikin wannan magana ta hadaka dumu-dumu, ciki harda, Rotimi Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, sa’annan akwai mutane da yawa daga Kudancin Nijeriya da ke kan harkar.