Shugaban hukumar ICPC, mai yaki da cin hanci a Nijeriya Dr Musa Aliyu ya ce hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 20 da wasu kadarori daga hannun wadanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa a shekarar 2024.
Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Litinin dinnan a birnin Ilorin yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a wurin taron manyan lauyoyin gwamnati a shiyyar Arewa ta tsakiya.
Taron an yi shi ne don inganta dabarun yaki da cin hanci da rashawa a kasa a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Aliyu ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba a matakin tarayya kadai ba ne, har ma a kananan hukumomi, don haka dole sai an maganceshi ta hanyar fitowa da sabbin dabaru.