DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi tir da kisan da aka yi wa wasu matafiya 12 da suka fito daga jihar Kaduna

-

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yi Allah-wadai da ajalin matafiya 12 ‘yan jihar Kaduna da wasu suka yi a jihar Filato yayin da suke tafiya daurin aure a karamar hukumar Pan da ke jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar Litinin dinnan, Shugaban kungiyar Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua, ya bayyana harin a matsayin rashin rashin imani, yana mai jaddada cewa irin wannan mummunan tashe-tashen hankula na bukatar gaggauta yin abinda ya dace a kansu.

Google search engine

Ya jaddada cewa irin wannan kisa na rashin hankali da ake yi wa ‘yan kasa wayanda ba su ji ba ba su gani ba, abu ne da ba za a amince da shi ba, don haka akwai bukatar a dauki matakin gaggauwa dan kaucewa ci gaba da faruwar hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaban kasar Uganda mai shekaru 80, zai sake tsayawa takara bayan shafe shekara 39 kan mulki

Jam'iyyar NRM mai mulki a kasar Uganda ta ce shugaban kasar Yoweri Museveni zai sake neman tsayawa takara a zaben da za a gudanar a...

Hukumar zabe INEC da jam’iyyar PDP za su gana kan taron NEC a yau Talata

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC da jam’iyyar PDP za su yi wani zama don magance rikici tsakaninsu kan taron kwamitin zartaswa na...

Mafi Shahara